Kannywood

Zan so diyar ciki na tayi harkar fim – Sadiq Ahmad

Jarumin nan na fina-finan Hausa a masa’antar Kannywood mai suna Sadiq Ahmad ya bayyana cewa shi zai so diyar sa ta yi harkar fim don bai ga wani abu ba a cikin ta.

arumin ya bayyana haka ne a yayin da yayi wata fira da majiyar mu dake wallafa mujallar da ta jibanci harkar fim a watannin baya.

Jarumin yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake ansa wata tambaya da aka yi masa game da ko zai iya barin diyar sa ta cikin sa tayi harkar fim.

A ansar da jarumin ya bayar kuwa ya bayyana cewa tabbas zai iya barin ta domin kwa ba wani abu bane.

“E, zan iya barin ta ta yi. Ai ba wani abu bane,” in ji shi.

Sai dai kuma ya bayyana cewa ba zai tursasa mata ba wajen cewa dole sai ta yi fim din ba inda yace duk abun da take so shine za ta yi.

A cewar sa: ” Kasan bahaushe yace ka haifi mutum, baka haifi halin sa ba; za ta iya yiwuwa na ce tayi amma ita kuma tace burin ta ta zama lauya ko likita, kaga kenan babu yadda zan yi da ita.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×