Labaran Duniya

Yan Mata! Kada Ku Baiwa Namiji Soyayyarku Har Sai Ya Amsa Muku Wadannan Tambayoyin

Kamin namiji daya yayi kuka mace ta yaudaresa, sai na samu mata akalla guda goma sun mini kokarafin maza sun yaudaresu.

Mata kalilan ne- suke iya sarrafa maza yadda ya kamata ba yaudaresu ba. Suna yin hakan ne kuwa saboda yadda suke amfani da hankali a lokutansu na soyayya ba da zuciyarsu ba.

Wannan darasin zamu kawowa mata wasu tambabyoyin da yakamata tayiwa dukkanin namijin dayake sonta da aure kamin saki jiki da shi.

Duk namijin da yace miki yana sonki da aure, tabbas yana da hujjarsa na yin hakan. Don haka ki tambayeshi mai yasa yake sonki duk kuwa da miliyoyin mata a wannan duniyan.

Anna amsar da zai baki zai tabbatar miki da gaske yake ko kuma wasa ya zo yi.

Ba hujja bane namiji yace miki haka nan kawai yaji yana sonki, a neman mace irin na aure dole ya zama akwai hujja mai .

Idan namijin da yake sonki da aure yana da mata, ki tambayeshi dalilin da yasa yake son kara aure.

Idan kuma bai da aure tambayeshi ko yana da budurwa a yanzu idan Kuma rabuwa suka yi da budurwar tasa tambayeshi abunda ya rabasu.

Dole ne namijin da zai kara aure ya zama yanada gamshenshiyar hujjar karawa.

Idan kuma ya taba yin soyayya da wata dole akwai abunda ya hadasu.

Don haka samun wannan amsar tambayan yana da kyau.

Tambayeshi a tunaninsa mai yake kara dankon soyayya masoya har suji mutuwace kadai zata rabasu.
Amsar wannan tambayar zai haska miki ko wannan yama san inda soyayya ya dosa kodai yazo bata miki lokaci ne.

Koda addininki daya da wanda yake son aurenki, ki tambayeshi akidarsa.
Mutane da dama sun fi fifita kaunarsu akan akidunsu da kungiyoyiinsu na addini fiye da shi kansa addinin.
Don haka sani akidar nutuma addinance zai yi matukar taimakamiki na amince masa ko kaurace masa.

Yiwa mai sonki da aure tambaya kai tsaye akan haihuwa domin jin irin ra’ayinsa da tunaninsa akan haihuwa.
Akwai mazan da kwata kwata basa son su haihu. Akwai masu kyaade yawan abunda suke son haifa. A kwai kuma masu Dan Karen son tara ‘ya’ya a rayuwarsu.
Don haka saurari irin amsar da zai baki domin sanin mataki na gaba.

Akwai mazan da basu son ganin macen da suka aura tana aiki ko sana’a koma kasuwanci.
Yi kokarin ya amsa miki wannan tambayar na ko zai iya barin matarsa tayi aiki, sana’a ko kasuwanci.

Yi tambayi mai sonki da aure game da abokansa, da kuma girman iyalansa.
Sannin wadannan abubuwan suna da kyau ga mace wajen wanda yake sonta da aure.

Domin shirin yadda zata yi mu’amala dasu.

Kudi masifa ne a rayuwa, don haka tambayi mai sonki da aure yadda ya dauki kudi a rayuwansa.

Akwai mutanen da su bautawa kudi suke yi. Suna iya batawa da kowa a kan kudi. Kuma suna iya daure ko na kusa dasu ne muddin takadama na kudi ya hadasu.

Baya ga sanin matsayinsa game da kudi, dole ne ki san abunda mai sonki da aure da yake yi a rayuwarsa.

Sanin sana’ar sa, aikinsa ko Kasuwancinsa ya zama dole a waje ki domin gano ko zaki iya auren irinsa.

Kada ki kammala masa tambayoyin nan ba tare da sanin abubuwa da suke dadada masa ba da kuma abubuwan da suke bakanta masa.

Saninsu yana da amfani koda kuwa ba amincewa Zaki yi da shi ba. Gaba amsar zai miki amfani kila cikin abubuwan da yake so ke kuma kin tsanesu. Ko abunda yake ki ke kuma akwai abunda bazaki iya dainawa ba.

Shi soyayar aure ba iri guda yake da soyayyar soyewa ba. Na aure mataki mataki ake kaiwa kamin sakin jiki da juna. Amma soyayar soyewa nan take ake yi a kuma gama.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×