

Wata kyakkyawar budurwa tayi yinkurin kashe kanta saboda wani bidiyo da ake zargin itace a ciki tana kashi a kusa da wani tsohon gida wanda ake kira da (Kango).
A yadda rahoto yazo wannan budurwa suna tare da saurayinta ne a cikin mota suna tafiya sai cikin ta ya kulle irin wannan kashin wanda baya baka damar rike shu ya same ta.
Sai ta nema saurayin nata da ya tsaya ta dan shi wannan tsohon gidan domin rage cikinta saboda bata iya rike shi, ta shiga wannan gida tsohon gida tayi kashin ta, ta fito suka tafi.
Bayan wasu tsawon lokuta kwatsam take jin labarin an ga bidiyon tana kashe a daji yana yawo a shafukan sada zumunta. Da taji bata iya daukar abun kunyar shiyasa tayi yinkurin kashe kanta din.
A rahoton da wannan budurwa ta bada ta tabbar babu wanda yake a wannan wajen domin da akwai zirga-zirgar mutane bazata tsaya tayi anan ba, gara tayi shi a cikin wandonta yafi mata mutunci.
Ta bayyana tana zargin wannan saurayin nata da aikata wannan abu domin shi kadai ne a wajen kuma shine wanda yasan meta shiga yi, abinda yasa take tunanin shine saboda yanzu basu tare