
Yadda Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Ladan Ta Bayyana Irin Farin Cikin Da Take A Gidan Mijinta Bayan Shekara 9 Da Auren. Allah Ya Albarkaceta Da Haihuwa Yara Biyu Zuwa Uku.
Inda Suke Zaune Zaman Lafiya Da Angon Nata.
Tsohuwar Jarumar A Masana’antar KannyWood, Fati Ladan Ta Cika Shekaru Tara (9) Cif Cif A Dakin Mijinta Shetima. Jarumar Dai Tayi Aurenta Ne A Shekarar 2013, Inda Tunda Jarumar Tayi Aure Tayi Bankwana Da Masana’antar Ta Kannywood.
Kafin Fati Ladan Din Tayi Aure, Jaruma Ce Da Taja Ragamar Manya Manyan Fina Finan KannyWood, Wanda A Wancan Lokacin Tauraruwarta Tana Haskakawa Sosai.