News

Yadda Asirin Wani Tsoho Ya Tonu Da Yake Lalata Da Matan Aure Akan Zai Basu Maganin Mallakar Miji

Mun samu labarin dubun wani ya cika bayan kwashe shekaru da yayi yana lalata da matan aure akan zai basu maganin mallakar miji. A yau mun samu rahoton wani dattijo yana yaudarar mata da sunan ba su sirrin mallakar miji.

Ya kasance yana kwana da su, a kwanakin nan asirinsa ya tonu.

Mun samu wannan rahoto daga DCP Abdullahi Kiyawa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, wanda shi ma ya ce an kama shi ne saboda wata yarinya da ta nemi taimakonsa.

Yana kwana da ita daga baya yarinyar ta kai kararsa wurin ’yan sanda ta kuma yi mata bayanin abin da ya yi mata. Bayan samun wannan bayanin ba su yi kasa a gwiwa ba suka kai wannan yarinya domin nuna musu kauyen da yake zaune da kuma gidansa.

Sun yi nasarar kama shi har ma sun yi masa faifan bidiyo suna neman ya bayyana wa duniya da kansa wannan mugunyar laifin da ya aikata.

Mun kawo maku wannan bidiyon ga masu bukatar kallo gashinan:

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×