Kannywood

Wata Sabuwa: Rahama Sadau Tasake Kwaba A Kafar Sadar Ta Zamani

Lamariń ya biyò bayań wani faifan bidiyònta ne da aka gan ta a ciki tana cewa a kashe karatun Alkur’àní a cikiń mòtarta a sa mata wàka.

Aminiyà ta bi diddigin bidiyon, inda ta ganò cèwa lamarin ya faru ne a cikin fim din Nadiya na jarumar, inda ta fito a matsayin matar Umar M. Shareef.Rahama Sadau Ta Sakè Tayar Da Kùra À Kafafeń Yada Labaraí Na Zamaní

A cikin fim din, jarumar ta fito a matsayin ’yar Rabi’u Rikadawa wanda ya fitò a matsayin mai dukiya sosai ya shagwaba ’yarsa wato Rahama a fim din.

Wannań ya sa ta yi aùre, amma ko wankan janaba da Sallah ba ta iya ba, sannan ba ta iya girka abinci ba, inda har ta kunya ta angonta a gaban abokansa da ya gayyata domin su ci abinci matarsa wayayya, amma suka kasa cin abincin saboda rashin dadinsa.

Daidaí wajeń da ya jawò maganà, a daidai minti na 26 ne na fim din, jarumar ta fita a mòta tarè da direbanta mai suna Habu, inda a cikin mòtar yake sauraron karatuń Alkur’ani, sai ta cè ya cire ya sa mata waka.

Da ya tambayè ta ta fi son wakar a kan karatun, sai ta ce, “Ban sani ba, kuma ban damu ba,” cikin harshen Ingilishi.

A wani faifan bidiyo da Sheikh Muhammad Auwal Maishago Zariya ya yada na wani malami, ya rubuta cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah mun tuba, Allah kada ka kama mu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”

A cikin bidiyon, malamin ya ce, “Hasbunallahu wa ni’imal wakil. Kun dai kalli bidiyon da ke kusa da ni da ’yar fim din Hausa mai suna Rahama Sadau ta yi, inda ta ce a cire Kur’ani a saka mata kida kuma ta yi tsaki kuma aka yi bidiyo aka yada saboda rashin kunya da rashin ladabi.

“To wallahi ita wannan ’yar fim Rahama Sadau muna jan hankalinta, ta yi gaggawar nadama ta koma zuwa ga Allah ta yi kuka ta yi takaici ta nemi Ya yafe mata.

“Idan ba haka ba, to wallahi ana jiye mata bala’i da wata masifa da za su iya riskarta tun a nan duniya saboda Kur’ani ba a yi masa rashin ladabi a kai labari.”

Da take mayar da martani a kasan rubutun, jarumar ta rubuta cewa, “Alaramma ai da ka kalli duka fim din kafin ka yi raddi a kai. Maganarka akwai rashin adalci a ciki.”

Shi kuma wani mai suna Sulaiman Iyali, wanda da alama masoyin jarumar ce, sai ya yi mata martani da cewa, “Tawa gaskiya, ya kamata mu tsaya a inda aka umarce mu da kuma inda aka hane mu. Domin addini da Alkur’ani ba ababen wasa ba ne. Allah (SWT) Ya sa mu dace.”

Wani mai suna Auwal Parruk ya ce, “Rahama Sadau maganarki haka take amma shawarata a matsayinki ta Musulma kuma mai kishin Musulunci ba kowace rawa za a baki ki hau ba, domin kuwa akwai abin da idan kika yi shi kin san dole a zarge ki kuma a matsayinki na Musulma addini ma bai yaddar ki rika yin abin da dole zai zama abin zargi gare ki ba. Allah Ya sa mu dace duniya da Lahira, amin.”

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×