Labaran Duniya

Wasu Dalilan Da Suke Sawa Gaban Mata Yake Bushewa

Akwai matan da suke da matsalar bushewar gaba a yayin da suke tsaka da kwanciyar aure.

Hakan kuwa yakan jawo musu na kasu ta hanyar zamantakewar auratayyarsu da mazajensu.


A darusan mu na baya, mun yi bayanin irin yadda ruwan gaban mace yake da tasiri da alfanu a jikinta, baya ga kariya ne daga cututtukan da zasu iya shiga gabanta, haka nan yana karawa mace ni’imar dake jiyar da namiji dadin matarsa.

Ga wasu matsaloli ko cutukan da suke jawowa gaban mace ya rika daskarewa ana saduwa da ita.

1:Vaginitis: Wannan wani infection ne da take shiga gaban mata ta jawo musu bushewar gaba.

Haka nan kuma mace zata rika jin zafi idan ana saduwa da ita.

Duk wata mace dake fuskantar irin wannan matsalar to tayi maza ta tuntubi likita.

2: Vaginalism practices: ita kuma wannan kwayar cutar idan ta shiga gaban mace tana tsuke mata gaba ne yadda azzakari bazai shiga cikin sauki ba, saboda yadda gaban ya kankan ce kuma ya daskare babu ruwa a ciki.

3:menopause: A lokacin da mace ta daina al’ada, a wannan lokacin sha’awar ta yana daukewa. Wannan rashin sha’awa yana ya kansa ruwan gabanta ya dauke.

Idan ruwan gabanta ya dauke sai kuma gabanta a tsuke.

Sakamakon hakan idan za a yi Jima’i da nacen data daina al’ada dole ne a sameta a bushe saboda wadannan matsalolin da muka ambata a sama.

4:Sjögren’s syndrome: Duk wata mace mai wannan cutar yana da wuya ayi saduwar mintuna uku da ita gabanta bai dawo ya daskare ba.

Idan mace na fama da wannan cutar za a sameta babu ruwa sosai a jikinta, bata yin gumi, ko hawaye bai digowa daga idanuwan ta.

Wasu Dalilan Da Suke Sawa Gaban Mata Yake Bushewa
Wasu Dalilan Da Suke Sawa Gaban Mata Yake Bushewa

5: Rashin Cin Abinci Masu Kyau: Macen da bata samun abinci masu gina jiki, ko yinwa ya addabeta, wannan matar ba za a iya samun ruwa a gabanta ba.

Koda an samu bazata jima ba gaban nata zai shanye.

6:Rashin Natsuwa: Muddin za a yi Jima’i da mace a cikin rashin natsuwa, to ba za a sameta da ni’ima ba. Mace komai lafiyar ta, duk irin abinci mai kyau da zata ci muddin za a yi Jima’i da ita ba cikin natsuwa ba ita ma ba za a sameta da ni’ima ba.

Mace idan tana cikin natsuwa kuma hankalinta a kwance, tabbas za a sameta yadda namiji yake son a jita.


7:Rashin Soyayya Ko Sha’awa: Idan namijin da mace bata sonshi zai yi Jima’i da ita zai sameta bata da sha’awar sa.

Rashin wannan sha’awar nasa zai hana ni’imar jikinta bayyana. Rashin bayyanar ni’imar ta kuma zai sa gabanta ya bushe.

Wadannan sune wasu cutuka da yanayin da zasu iya jawo gaban mace ya bushe kamin ko lokacin da ake tsaka da kwanciyar aure da ita. Don haka matsaloli da za aga likita a kansu ya zama wajibi mace ta hanzarta ganin likita, wanda kuma yanayin ta ne zai jawo mata waraka sai tayi hakan.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×