
Wani magidanci ya cinnawa ƴaƴan matar sa guda biyar wuta bayan ta hana shi su yi kwanciyar aure.

Magidancin mai suna Ojo Joseph mai shekara 54 a duniya ya aikata wannan aika-aikar ne a jihar Ondo.
Lamarin ya auku ne a unguwar Fagun cikin garin Ondo a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoɓan 2022 da safe.
Majiyar mu ta shafin Labarunhausa ta rahoto.
Yadda magidancin ya aikata wannan ɗanyen aikin, Joseph ya fusata ne inda ya cinnawa yaran wuta bayan mahaifiyar su ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure.
Wanda ake zargin ya watsa man fetur a ɗakin da yaran ke yin barci sannan ya cinna masa wuta.
Ɗaya daga cikin yaran ya ƙone har lahira yayin da sauran suka samu munanan raunika inda ake duba lafiyar su a babban asibitin tarayya dake Owo. Matar sa da tagwayen da suka haifa tare masu watanni sha takwas a duniya sun tsira daga wutar da ƴan ƙananan raunika.
Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da take tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta bayyana cewa tuni aka kama magidancin.
Ta kuma ƙara da cewa an fara gudanar da bincike sannan za a kammala kafin a tura wanda ake zargin zuwa kotu bisa zargin sa wuta da kisan kai.
Abuja – Wata mazauniyar burnin tarayya Abuje dake faɗi tashin zama uwa tana neman kyakkyawan mutumin da zai iya sanya wa ta ɗauki ciki.