
Wani bidiyon babban abun mamaki yana ta yawo a social midiya na wata budurwa da take da baiwar iya daukar abu mai nauyi da mazaunanta harta dinga yawo dasu ba tare da sun fadi kasa ba.
Wannan budurwa tunda ta manyanta mazaunan ta suma sukayu girma tun daga wannan lokacin ta lura zata iya daukar komai da abunta taje inda take so ta dade tana daukar abubuwa amma babu wanda ya taba nuna wannan baiwar ta ta wa duniya.
Sai rana daya wani Mai bidiyoyin barkwanci ya nema da yana so suyi bidiyo wannan bidiyon shine wanda a cikin dan karat n lokaci ya zagaye duniya kowa yana mamakin yadda wajen yake da taushi sannan babu kashi taya take iya rike abu dashi.
Bare kuma har mutum kamar wannan mai girma ya hau ta diga yawo dashi a wannan bidiyon wanda ya hau mazaunanta shine mai wasan barkwancin. Domin ayi dariya shiyasa shima bayan ta sauke shi yake kokarin daura wata macce kan nashi shima ya jaraba ko zai iya.
Amma abun dariya shine babu ma inda zata daura kafarta saboda a shafe yake nashi. Hakan yasa mutane dariya kamar yadda yayi saboda ayi dariyar.