Kannywood

Tirkashi: Rikici Ya Barke Tsakanin Tsohuwar Matar Adam Zango da Yan TikTok

Amina itace matar da Adam Zango daya fara Aure a Rayuwar shi itace Mahaifiyar danshi na farko Aliyu wanda akema lakabi da haidar, wanda daga karshe dai Zaman bai dade ba suka rabu.

Tun bayan rabuwar Adam Zango da matarsa ta shida watau safiya chalawa, Sai Mutane suka mayar da hanakalinsu akan Tsohuwar matarshi ta farko watau Amina inda suke rokon yakamata ya maidata dakinta tun harma da da a Tsakanin su.

Amina ta kasance me Sha’awar harkar Finafinai tun kafin Auren su da Adam Zango a wata hira da akayi da ita ta bayyana cewa har Finafinan kudancin Nigeria ta farayi, bayan Auren su da adam zango suka haifi dansu Haidar daga nan sai auren ya mutu wanda har yau dai babu wanda yasan dalili rabuwar tasu.

A Yanzu haka Amina ta dawoMasana’antar Kannywood inda ta fara fitowa acikin shiri me dogon Zango Gidan Danja, Sai dai Kuma a kwanakin nan anata samun rikici Tsakanin ta da Masu bibiyar ta a Shafin ta na TikTok inda abun yayi kamari Har ana hadawa da Zage zage.

 

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×