Kannywood

Taƙaitacen tarihin Abdul M Shareef da gudumuwarsa a kannywwod

  1. Sani hamza funtua dan jaridar gidan jaridar legit ya kawo taƙaitaccen tarihin abdul aziz Muhammad shareef wanda anka fi sani da Abdul m shareef irin yadda ya bada gudunmawa a masana’antar kannywood.

Jarumi Abdul’aziz Mohammed Shareef ya cika shekaru 36 a duniya.

A shekarar 2012 @abdulmshareef ya ajiye sana’ar waƙa, ya koma harkar fina finai gadan gadan, inda ya shiga da ƙafar dama, domin ya shahara cikin karamin lokaci.

Ya fito a cikin fina finai da dama, amma wanda ya fara haska shi shine fim din Makashinta wanda @tijjaniasase_real ya shirya.

Kadan daga cikin shirye shiryen da ya fito:

– Da Ace Babu Zuciya, Wuff
– Karshen Mujadala, Makashinta
– Yar Agadez, Dattijo, Ali Baba
– Gamu Nan Dai, Bana Bakwai
– Hawaye Na, Ba Zan Barki Ba
– Garwashi, Kaddara, Jani-Muje
– Rayuwarmu, da sauransu.

Abdul na da yan uwa biyu da ke a cikin wannan masana’anta ta Kannywood; @umarmshareef da kuma @mustaphamshareef9531

Jarumi Abdul M Shareef na da aure har ya haifi yara Hudu, maza uku da mace daya

Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×