
Labarina shiri ne mai dogon zango da ke karkashin masana’atar Kannywood wanda kuma ya samu karbuwa sosai a wajen mutane wanda gidan talabijin na arewa24tv ke haskawa a duk bayan sati daya wanda ake sanyawa ranar juma’a da misalin karfe takwas tun daga zango na farko har zuwa zango na hudu.
A yau kuma an sake dawowa tafiya dogon hutun da ankayi bisa tsayawa aikin wannan shirin tare da maye gurbin wasu jarumai da bazasu sake haskawa a fim din ba duba da kwantaraginsu ya kare.