
Abinda yake faruwa a zamantakewar aure, shi namiji abokanansa za su ziga shi musamman a ranarsu ta aure, za su ce sai ya nuna mata shi namiji ne, da haka ne baza ta rainaka ba, ita kuma za ace kada ki yi saurin yarda dashi sabida kada yace daman kin saba a waje. To dukkanin waɗannan abubuwa biyun cutarwa ne. A inda matsalar take, shi namiji a daren farko sha’awarsa za ta ziga shi cewa sai ya sadu da matarsa da ƙarfi, to ita kuma jikinta a haɗe yake, kaga kenan zai cutar da ita tunda bata taɓa yi ba, sabida zafi za taji, kuma duk ranar da zai sake saduwa da ita, to wannan tunanin zafin zaiyi tasiri a cikin zuciyarta, dalilin hakan sai yasa ta dinga jin tsoron saduwar”
“Kada kayi gaggawar nemanta da jima’i a ranar farko, ka daure ka haƙurtar da zuciyarka har na misalin wasu ƴan kwanaki baka nemeta da jima’i ba, ka danne sha’awarka, idan kayi haƙuri to ita da kanta za ta nemeka. Amma babu komai don ka taɓa jikinta taɓawa irin ta sha’awa, haƙiƙa wannan bazai sa ta tsorata da kai ba, saidai ma ya ƙara mata ƙaunarka, tabbas idan kukayi tsawon kwanaki uku a haka to ita da kanta za ta kawo maka kanta, kaga kenan baka cusa mata tsoron jima’in ba, amma idan wancan yanayin farkon ne, to haƙiƙa saidai kai ka dinga nemanta, amma ita baza ta nemeka ba sabida tun a ranar farko ka tsoratar da ita ta hanyar yin jima’i da ita mai zafi”
Da yawan mazaje burinsu a ranar farkon su ta aure suga sun zaƙƙema matansu, wanda hakan kuma ba ƙaramin cutar da matan yake yi ba, wasu a sanya musu fargaba, wasu a cusa musu tsoron jima’in, wasu kuma a raunata su”
–
Kuyi Comment