Labaran Duniya

Sabuwar Hanyar Da Mutane Ke Satar Account Na Whatsapp Din Mutane Cikin Sauki A Wannan Shekarar Ta 2022.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaku Kare Account Dinku Na Whatsapp Cikin Sauki Daga Barayi Sannan Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wata Sabuwar Hanya Da Barayin Kebi Su Sankamewa Wanda Bashi Da Wayo Da Kuma Tunani Account.

Abinda Muke Bukata Shine Ku Karanta Wannan Bayani A Nutse Tun Daga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Wannan Bayani Dalla-dalla.

To Da Farko Dai Kamar Yadda Kuka Sani Manhajar Whasapp, Wata Manhaja Ce Da Ake Aika Sako Ta Cikinka Ga Duk Wani Mutum Dake Duniya Matukar Yayi Register Na Wannan Application.

Sannan Wannan Manhaja Tana Da Saukin Cin Kudi Wurin Tura Sako Ga Duk Wani Mutum Da Kake Bukatar Turawa Sako A Fadin Duniya.

Manhajar Whasapp Tana Dauke Da Wasu Sirrika Da Dama Wadanda Hatta Wanda Yayi Register Baisan Dasuba.

A Binciken Da Mukayi Mungano Cewar Kadan Ne Daga Cikin Masu Amfani Da Wannan Manhaja Suka San Wasu Sirrikan Whatsapp.

To Wadannan Sirrika Dai Sun Hada Da 2step Verification, Dakuma Dora Fingerprint, saboda tsaro.

To Kasancewar Ba Kowane Yasan Yadda Ake Saita Wadannan Abubuwa Ba Yasa Wasu Daga Cikin Mutane Suke Amfani Da Wannan Hanya Wajen Sace Musu Account.

Barayin Suna Amfani Da Hanyar 2step Verification Su Dara Gmail Account Dinsu Akan Account Dinka Suna Amfani Da Whatsapp Dinka Koda Basu Da Numbar Ka.

Hanyar Da Sukebi Itace Zasuyi Request Na Code Sai Su Kira Number Din Wayarka Sucema An Bude Group Na Makaranta Anaso Asaka Ka Acikin Wannan Group Saboda Haka Akwai Wani Code Da Aka Turo Kabasu Wadannan Numbobi.

To Da Zarar Kabasu Shikenan Take Zakaga Anyi Waje Dakai, Sannan Suna Bin Hanyoyi Masu Yawa Domin Karban Account Din Mutum, Mafita Dayace Duk Wanda Yace Kabashi Wani Code Ko Numbobi To Kadda Ka Kuskura Ka Bashi, Domin Kana Bashi Sunanka Gawa.

To Wannan Dai A Takaice Itace Sabuwar Hanyar Da Yan Damfarar Kebi Wurin Karban Account Din Whatsapp Din Mutane Cikin Sauki.

Mungode Mungode Mungode Da Kasancewa Da Shafin Hikimatv Da Kukayi Inda Muke Fatan Zaku Danna Alamar Notification Domin Sanar Daku Da Zarar Munsaki Sabbin Darusa A Kowane Lokaci

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×