Uncategorized

Nafisa Abdullahi ce tafi fice a Google 2023

Nafisa Abdullahi
Bayanan hoto,Nafisa tauraruwar fim ɗin Labarina, ita kaɗai ce ‘yar Kannywood da ke cikin 10 na farko mafiya shahara a Google Search a 2021

Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi na cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-ɓata na Google Search a shekarar 2021 a Najeriya.

Tauraruwar ta fim ɗin Labarina ta shiga jerin ne tare da taurarin fim na kudancin Najeriya da ake kira Nollywood irin su Destiny Etiko da Tonto Dikeh da Zubby Michael.

Sai dai Google ya saka Nafisa a ɓangaren Nollywood maimakon Kannywood, wanda nan ne take ciki ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Ita ce a matsayi na shida a sashen taurarin fina-finai bayan Destiny Etiko da Zubby Michael da Pere da Tonto Dikeh da Iyabo Ojo da kuma Olu Jacobs.

Haka kuma, Nafisa ce kaɗai daga taurarin Kannywood da ta shiga cikin taurari 10 na farko a Google Search.

Sauran ‘yan Kannywood Rahama Sadau da Fati Washa da Maryam Yahaya da Hadiza Gabon ne ke biye mata a shahara, duk da cewa ba sa cikin goman farko.

Shafin Google kan fitar da kalmomi da sunaye da ababen girki da mutane waɗanda miliyoyin masu amfani da shafin suka fi bincikawa duk shekara.

Sannan shafin kan yi wa sunayen rukuni, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da ‘yan fim da fina-finan kansu da tambayoyin da aka fi yi.

Nafisa na da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a Facebook.

A ɓangaren fina-finai, ‘yan Najeriya sun fi neman bayanai kan Squid Game da Coming to America 2 da Sex Life da Black Widow da kuma Red Notice.

Daga cikin waɗanda suka rasu a 2021 kuwa, shahararren malamin Kirista TB Joshua da mawaƙi Sound Sultan da kuma Sani Dangote – ƙani ga Aliko Dangote – na cikin waɗanda aka fi dubawa.

Matakan shaharar Nafisa

Nafisa Abdullahi

Kamar yadda bayanai suka nuna, Nafisa ta fara shahara ne a shafin daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janairun 2021.

Hakan ba zai rasa nasaba ba da kammala kashi na 2 na fim ɗinta mai dogon zango wato Labarina, inda aka haska zangon ƙarshe a ƙarshen watan Disamban 2020.

Masu neman bayanai kan tauraruwar sun ƙaru zuwa kashi 93 a watan Satumba, wanda a daidai lokacin ne ake tsaka da haska kashi na 3 na Labarina.

Bugu da ƙari, masu bincika Nafisa Abdullahi sun ƙaru zuwa kashi 100 cikin 100 daga 5 zuwa 11 na watan Disamba. Wannan kuma idan ba ku manta ba, yana da nasaba da kayayyakin ƙawa da ta ƙaddamar mai suna NAFCOSMETICS.

Mazauna Abuja babban birnin Najeriya ne suka fi neman bayanai game da Nafisa, sai kuma jihohin Rivers da Legas da Kaduna.

Sirrin shaharar Nafisa

Nafisa Abdullahi
Nafisa Abdullahi ta kwana biyu ba a ganinta a harkar fina-finai kafin fara haska fim ɗin Labarina a 2020.

Fim ɗin wanda kamfanin Saira Movies na Aminu Saira ke shiryawa, ya samu Nafisa a matsayin babbar jaruma wadda aka gina labarin a kanta.

Tun bayan fara haska Labarina babu wani fim da Nafisa ta fito a ciki wanda ya yi kusa da farin jinin da Labarina ke da shi.

Yayin da tauraruwarta ke tsaka da haskakawa, ta ƙaddamar da sabon kamfanin kayan kwalliyarta mai suna NAFCOSMETICS a watan Nuwamban 2021.

Kayan kwalliya
Bayanan hoto,Nafisa ta ƙaddamar da kamfanin kayan kwalliyarta mai suna NAFCOSMETICS a watan Nuwamba

Bugu da ƙari, an san tauraruwar da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen Turai da Amurka, inda takan je domin ƙarin karatu ko kuma yawon buɗe-ido.

Tattara bayyani mun dauko daga Bbchausa

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×