Labaran Duniya

Mutuwar Amarya Bayan An gama Daura Auren Ta Yayi Matukar Girgiza Mutane

Allah Sarki Mutuwar Amrya Bayan An gama Daura Auren ta Yanzu Tayi Matukar Girgiza Al’umma Sosai Wata amarya ta rigamu gidan gaskiya kwanaki kaɗan bayan tayi aure.

Angon amaryar mai suna Idris Elmustapha Daja, shine ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin sa Facebook. Shafin Linda ikeji ya rahoto.

El-Mustapha Daja ya auri amaryarsa mai suna Maryam Muhammad Liman, a ranar 6 ga watan Janairun 2023, inda ta amaryar ta rigamu gidan gaskiya a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.

An yi jana’izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidan Hajiya Fatima Madugu, dakw akan hanyar Okada, cikin birnin Minna da safiyar ranar Laraba.

Sannan aka kai ta a makwancinta na gaskiya a maƙarbartar Gbakungu cikin birnin na Minna.

“Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun. Kwana sha ɗaya da aure, yau na rasa ta. Allah ya jiƙan ki da rahama ya sanya aljannah Firdausi ta zama makoma a gare ki.” Idris ya rubuta a Facebook.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×