Kannywood

Subhanallah: Ta Faru ta kare : Adam Zango ya saki matarsa

Bayan kwashe watanni bata gidansa bisa yajin da ta yi, daga karshe dai auren jarumin Kannywood Adam A. Zango ya mutu da matarsa Safiyya Umar Chalawa.Ta Faru ta kare : Adam Zango ya saki matarsa

Sai dai duk da cewa ba saki uku ya yi mata ba, amma majiyarmu ta Mujjalar Fim ta ruwaito tun can akwai saki daya a tsakaninsu tun ta na amarya, yanzu kuma ya sake aika mata da na biyu a gidansu da ke Birnin Kebbi.

A farkon wannan shekarar ne Adam Zango ya sanarwa duniya yiwuwar rabuwarsu da Saffiyya bisa abin da ya kira da “kin bin umarninsa” da ta ke yi bayan ya gano tana wani kasuwancin intanet kuma ya hanata ta ki hanuwa.

Wannan shi ne auren jarumin na shida da ya mutu tsakanin shekarar 2006 da ya yi auren fari zuwa wannan shekarar.

Yanzu dai yana da yara bakwai uku mata hudu maza, wadanda kowanne daga cikinsu mahaifiyarsa daban.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×