Kannywood

Matan Kannywood mu kiyaye sanya Sutura mai nuna tsiraicin mu – Mama Daso

FITACCIYAR jaruma Saratu Giɗaɗo (Daso) ta jan hankalin ‘yan matan masana’antar finaginan Hausa na wannan zamani a kan saka ire-iren sutura masu nuna surar jikin su. Shafin fimmagazine na ruwaito

Daso ta wannan tsokacin ne lokacin da aka ba ta damar yin magana a taron saukar Alƙur’ani da yi wa ƙasa addu’a wanda mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya shirya a Kano a shekaranjiya Litinin.

Jarumar barkwancin ta yi amfani da wannan damar ta ce, “Ya kamata mu mutunta kan mu a duk inda mu ke. Haka kuma don Allah mu kiyaye saka suturar da zai nuna tsiraicin mu, musamman ‘yan matan mu na wannan zamani. Hakan ba daidai ba ne, mu kiyaye.”

Matan Kannywood mu kiyaye sanya Sutura mai nuna tsiraicin mu - Mama Daso

Daso ta yi addu’ar Allah ya ƙara kare su daga sharrin mahassada da maƙiya.

Mujallar ta yi nazarin cewa ba tun yau ba ake magana kan yadda wasu daga cikin jarumai mata su ke shiga mai nuna surar jikin su, wanda ya sa su na shan suka a wurin jama’a.

Ba ‘yan fim ne kaɗai ke yin wannan ɗabi’ar ba, amma ganin cewa su sanannu ne ya sa ake ɗora dukkan laifin a kan su.

Sannan kuma su na iƙirarin cewa su faɗakarwa su ke, kenan su malamai ne a cikin al’umma, tunda jama’a na kwaikwayon wasu abubuwan da su ke nunawa a finafinan su, amma duk da haka ba su kiyaye abin da zai zubar masu da ƙima a idon al’umma.

Yawancin malamai idan su na wa’azi su kan yi misali da wasu abubuwa da ‘yan fim su ke yi, musamman mata.

A matsayin su na masu faɗakarwa, bai kamata a ce su na shiga irin wanda zai nuna surar jikin su ko wani ɓangare na jikin su ba, domin ko a rayuwar su ta zahiri ba ta fim ba wasu daga cikin su haka su ke saka sutura mai nuna surar su.

Misali, akwai lokacin da jaruma Fati Washa ta saka wata rigar ‘yan ƙwallon Nijeriya, wanda ba ta saka rigar mama a ciki ba, har kan maman ya fito ƙuru-ƙuru ana ganin alamar sa.A lokacin babu irin maganar da ba a yi ba soshiyal midiya.

Ita ma jaruma Maryam Yahaya a ‘yan wasu watannin baya, bayan ta tashi daga rashin lafiya ta tafi ƙasar Dubai shaƙatawa, ita ma ta yi hotuna sanye da kayan da su ka nuna kan maman ta ba rigar mama a ciki.

Hotuna sun jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, har wasu na faɗin cewa jarumar kwanan nan ta tashi daga rashin lafiya amma jinyar da ta yi ba ta sa ta yi hankali ba.

Ganin irin abu da ke faruwa ne, musamman ga jarumai mata na wannan zamani, ya sa Daso ta yi wannan tsokacin.

 

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×