News

Lawan Ahmad Yasha Zagi Da Baƙaƙen Kalamai Daga Mabiyansa Bayan Neman Taimakon Kudi Dayayi Daga Wajensu

Kamar Yadda Kuka Sani A Yanzu Ana Tsaka Da Tattauna Wani Al’amari Game Da Neman Taimako Da Manyan Jaruman Kannywood Sukeyi, Biyo Bayan Koyi Da Wani Mawakin Kudanchi Wato Davido.

Acikin Satin Nan Ne Mawaki Davido Bukaci Mabiyansa Dasu Tura Masa Kudi kimanin Miliyan Daya-daya Ga Dukkan Abokan Aikinsa, Aikuwa Ba’a Kai Awa Ashirin Da Hudu Ba, Abokansa Nasa Suka Hada Masa Wajen Naira Miliyan Dari Biyu Da Wani Abu.

Sai Dai Abun Ya Janyo Cece-kuce Ganin Cewa Da Wahala Mutum Yayi Wata Sana’a Da zai Samu Wannan Kudi A Rana Daya, Baya Da Haka Wasu Ma Daga Cikin Mawaka Kamar Su Psquare Da Sauransu Sun Bukaci Kamar Haka Daga Mabiyansu, Amma Abun Bai Ko Kama Kafar Na Davido Ba.

Bayan Wannan Abu Daya Faru A Kudanchi, Sai Jaruman Kannywood Suka so Suyi Koyi Da Abunda Mawaki Davido Yayi, Ganin Cewa Tunda Ya Bukaci Haka Daga Mabiyansa Kuma An Nuna Masa Kauna Sai Suke Ganin Hakan Zata Kasance Dasu.

Daga Cikin Jaruman Kannywood Dasuka Bukaci Haka Daga Mabiyansu Akwai Lawan Ahmad Fitaccen Jarumin Kannywood, Ya Bukaci Haka Daga Mabiyansa Yadda Wasu Suke Tura Masa Kudi, Wasu Kuma Sabanin Haka.

Yadda Acikin Mabiyan Nasa Wasu Har Bakaken Kalamai Suke Fada Masa Akan Wannan Abu Daya Nema, Duk Da Dai Jarumin Ba Wani Abu Yace Ba , Face Ataimaka Masa Suci Darajar Annabi Muhammad SAw Tare Da Rubuta Lambar Akawun Dinsa Na Banki Ajikin Bidiyon Kamar Haka.

Sai Dai Daga Cikin Mabiyan Jarumin Akwai Wadanda Suka Soki Maganarsa Kamar Yadda Muka Samu Daga Bangaren Tsokaci.

Toh Allah Ya Kyauta Zamu so Mu Karbi Ra’ayoyinku Akan Wannan Lamari Sannan Kuma Da Abunda Lawan Ahmad Ya Bukata Daga Masoyansa, Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×