Labaran Duniya

Ko Matarka Ta Gaske Ka Saka Ba Da Niyya Ba, To Ba Ta Saku Ba, Cewar Dakta Shareef Almuhajir

Dakta Sheriff Almuhajir, (Phd) Malami a Jami’ar Jihar Yobe kana kuma manajan daraktan Microfinance Bank, masanin harkokin tattalin arziƙi ta fuskar Islama, ya maida martani akan fatawar da Dakta Bashir Aliyu Umar da Dakta Ahmed Gumi suka yi na cewa “duk wanda ya saki matarsa a wasan kwaikwayo to matarsa ta gida ya saka”.

A tasa fahimtar, Dakta Muhajir ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne ace duk wanda ya saki matarsa a cikin wasan kwaikwayo wai matarsa ta gida ta saku. “Wannan ba gaskiya ba ne”

. Cewar Dakta Shariff.

Dakta Shariff ya bayyana hakan ne a ya yin tattaunawa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta hanyar wayar salula.

Dakta Shariff ya kafa hujja ne da hadisin manzon Allah (S.A.W) da ya ke cewa “Innamal a’amalu binniyyati”, “wato dukkan ayyuka ba sa tabbata sai da niyya.

A saboda haka, malamai da dama ciki har da Albani sun ƙaryata hadisin da ke cewa wai ba a wasa da ƴanta bawa da saki, ba gaskiya ba ne cewa idan ka sani matarka ta wasan kwaikwayo matarka ta gida ta saku, idan haka ne kenan matar da ka aura a wasan kwaikwayo ta zama matarka ?”

. Inji Dakta Sharif.

Dakta Shariff ya kuma buga misali da cewa idan ka nufaci yin jima’i da matar banza ba ka sani ba ashe matarka ce, to babu komai na zunubi a kan ka domin niyyar ka ta sha bamban da aikin da ka aikata.

Ba kamar yadda wasu malamai su ke ba da fatawar cewa akwai zunubin aikata zina a kan ka ba.

“Dazarar aiki bai zo daidai da niyya ba, to aiki ya rushe, haka nan idan niyya ba ta zo daidai da aiki ba, to niyya ta rushe”.Inji Dakta Shariff.

Daga nan sai Dakta Shariff ya ƙara da cewa ko da matarka ta auren gaske ka saka ba tare da niyya ba, to ba ta saku ba domin dukkan ayyuka ba sa tabbata sai da niyya dogaro da wancan hadisi na Manzon Allah (S.A.W), a saboda haka, “ina ba malamai shawara da su je su yi karatun fiqihu sosai”.

Cewar Dakta Shariff Almuhajir.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×