News

Innalillahi Yadda Miji Ya Kama Matansa Biyu Suna Madigo A Dakin Uwar Gida

20230201 091913

A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya samu matansa biyu da uwargida da amarya a matsayin masoyan juna cikin harkar ‘Madigo.’

Saninmu ne cewa a yau an wayi gari matsalar hulda tsakanin masu jinsi daya yana kutsowa cikin al’ummarmu. Har ta kai wasu kasashen duniya, musamman yammacin duniya sun fara yekuwar neman izinin auren jinsi daya.

Hakan ta sa sanya wasu tsirarrun ‘yan kasar nan a lokuta daban-daban su ma suke nemi su bi sahun wadansan la’anannun, wai suna neman gwamnatin kasar ta yarje musu auren jinsi daya, inda namiji zai auri dan’uwansa namiji, mace ma ta auri mace!

Tun kafin a je ko’ina ‘yan Nijeriya baki dayansu, suka fito fili suka yaki lamarin, su kansu masu madafun ikon kasar suka yi watsi da tayin da wasu shugabannin duniya suka yi. Ta tabbata dai babu yadda za a yi a amince da auren jinsi daya a Nijeriya.

Amma duk da haka, ba a rabu da bukar ba, aka haifi habu! Wadansu daga cikin al’ummarmu, ciki, har da Hausawa jefi jefi kan samu kansu a cikin wannan muguwar al’adar, inda za ka iske mace ta hakikice da ‘yar’uwarta mace, wai su masoya ne. Kwanan baya a Jihar Kaduna an kama wasu mata guda biyu da suka dambace bisa dalilin zargin juna da cin amana.

Ita ‘mijin’ ta fara kamar matarta (daya macen) da duka, har ta kai su ga caji ofis, inda suka fallasa yawan shekarun da suka yi tare a matsayin mata da miji, har da sadaki!

Dangane da hakan ne wani magidanci mai suna Abban Umma a nan Arewa ya bugo waya tare da aiko mana hotunan iyalinsa suna aikata muguwar dabi’ar ta madigo.

Magidancin mai kimamin shekaru 42, ya shaida mana dalla-dalla yadda lamarin ya faru, kana ya nuna mana hotunan yadda ya kama matan nasa

Sai dai mun shaida masa cewa ba za mu iya buga hotunan ba. Kana mun ba shi shawarar bai kamata a fallasa hakikanin sunayensu ba.

Malamin dai matafiyi ne, don kuwa yana daukar kayan gwari ne daga nan Arewa zuwa Kurmi, Ikko da sauran jihohin Kudancin kasar nan. A cewarsa, kafin ya kara mata sun jima tare da uwargida, don sun shafe akalla sukaru goma sha-daya tare da ‘ya’yansu hudu.

Amma a koda yaushe uwargidan sai mita take masa cewa yana yawan damunta. A takaice dai ya nuna cewa uwargidansa ba ta ba shi hadin kai wajen ibadar aure, wanda hakan ta sanya har ya kwadaitu ya kara aure.

Ba tare da jimawa ba kuwa ya kara auren wata matar suka zama biyu. Ya samu kansa cikin sabuwar rayuwa, gidansa ya koma tamkar ‘Aljannar duniya’. Ya nuna cewa sakamakon auren da ya kara, ita ma uwargidan ta kara zage dantse, ta rika daukar dukkanin bukatunsa.

Kishi ya fara kunno gidan, aka rika kai ruwa-rana. Hakan ta sanya sai da ya zage dantse wajen wanzar da zaman lafiya a gidansa. Daga bisani, kamar yadda ya ba mu labari sai komai ya lafa. Hadin kai a tsakaninsu ba kama hannun yaro.
Kafin ranar da dubun nasu ya cika, kullum sai ya rika lura cewa matan nasa kayansu iri daya. Sannan idan ranar girkin amarya ne, sai uwargida ta yi mata komai, sannan idan dare ya yi, sai ya yi da gaske zai iya kwana a dakin wadda ke girkin. Sai dai ya same ta a dakin dayar.

Sannu a hankali, ya fahimci ba sa fada a tsakaninsu, amma duk lokacin da ya shiga dakin wata, sai dayar ta rika kaiwa da kawowa a dakin har gari ya waye. Ba ya fahimtar komai! Idan kuma ya yi tafiya, duk sa’adda ya kira wayar kowacce zai fahimci tare suke, ko da cikin talatainin dare ne.

Abin ya fara damunsa don ‘ya’yansa ma aka daina kula su, sai ya dawo ya iske yara ba wanka ba wanki, ba tattalin zuwa makaranta da sauransu.

A kwana a tashi wata rana ya shirya yin tafiya sai mota ta ba shi matsala a bisa hanyarsa ta zuwa Kurmi. Tun kafin ya kai Abuja a daidai wani kuaye mai suna Katari.

Da ya fahimci motar ta samu babbar matsala sai ya yanke hukuncin komawa gida, Allah bar shi da safe ya taho da masu gyara su duba motar da kyau. Ya bar yaransa a motar ya koma.

Munsamo wannan labarinne  daga shafin 24blog.com.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×