Labaran Duniya

Innalillahi Kalli Yadda Wata Budurwa ta gudawa Malamin ta gaban ta yana kallah

Innalillahi Kalli Yadda Wata Budurwa ta gudawa Malamin ta gaban ta yana kallah
NASIHA GA YANMATA DA ZAWARAWA, MUSAMMAN MA GA YANMATA .

Ki kiyayi shan abin kara kiɓa domin yana kokarin zamo wa abin zargi a yau, ke da kika kasance nutsassiya, kiyi hakuri ko kina sha ki daina ki godewa ALLAH a matsayin da ya yi ki, in ba haka ba za ki ja wa kanki babban matsala musamman ta fuskar mutunci da kuma auruwa

Akwai yanmata da ba nutsassu ba sukanje su sha magani ko sanya abin hana ɗaukar ciki robar hannu, to wai yana sanya wasu jiki, shine sai yarinya tayi jiki ayi ta mamakin me ya sanya ta jiki, ko ayi ta cewa magani tasha ashe ashe …… Abinda yake gaskiyar magana biye biyen maza take wanda daman duk mace yarinya BUDURWA da take bin maza yanayin ta na sauyawa sosai to ga kuma in tayi planning yazo planning din tana daga cikin wa’enda yake sanyawa jiki.

Babban jan hankali ga yanmata masu irin wannan halin su ji tsoron ALLAH suna tuna mutuwa, yanzu har zamani ya kai yarinya ta zamo har da planning, ? Wannan musiba ce.

Abu na biyu yanmata wa’enda su ba aikata aikin banza suke ba ku ji tsoron ALLAH ku rufawa kanku asiri, in ba ki sha kada ki sha, in kina sha kidaina don yana da illa sosai ga lafiya, sa’annan kuma yanzu magana ta canja salo ke watakila ba ki daga cikin yanmata masu Ɗabi’ar yawon banza, maganin kiɓa kika sha azo ana zargin ki, ana bata miki suna.

Daga karshe ina jan hankali ga iyaye, yayyu, da yan uwa musulmi mu ji tsoron ALLAH muna kulawa da amanar ya’yan mu da kannai, da yan’uwa musulmi.

Maza kuma aji tsoron ALLAH, a daina shigar da ya’yan mutane harkar banza don wata sanadin lalacewarta daga yaudara ce, ku kuma mata adaina kwaɗayi da ɗaukar wa kai Rayuwa ta karya, a kame kai a fuskanci abinda zai amfanar da rayuwa a cire kwaɗayi da buri ayi aure, sai na canja waya ko sanya sutura da sauran kwaɗayi shi ke hallakar da mata, babu nutsuwa ko kwanciyar hankali da tunani mai kyau ga duk wanda ya auka irin Mummunar Ɗabi’ar nan, irin wa’ennan matsalolin ne ke hanawa yanmata aure, daga anzo neman aure abubuwa su lalace, ki natsu tun farko kiji tsoron ALLAH sai ki kalli kin gama yanmatanci lafiya, kin karatu, jin koyi sana’a, kinsamu miji kin yi aure.

Har cikin mata zawarawa akwai masu irin wannan Mummunar Ɗabi’ar yawanci irin matsalolin nan ma anfi samu ta wurin zawarawan, amma in Banda lalacewa na zamani me ya kai budurwa da wannan Ɗabi’a, nafi ambatan yanmata cikin nasihar ne saboda yadda suka kasance wasun su yara ne kuma ba su fahimci rayuwa ba sosai, kowa yaji tsoron ALLAH

A Wani Labarin Kuma

Batun Lalata Dan Yan Matan Jami’a Gaskiya Tayi Halinta

Abunda zan rubuta yanzu da yawa cikin Malaman jami’ah sun san haka yake, amma galibi kowa zai kauda kai ne saboda gudun zargi, ko kuma kar ace yana baiwa cutar da dalibai kariya. Duk da yiwuwar hakan, ba zai hanani bayyana abunda na sani ba, saboda shi ma wani ilimi ne da boye shi ya kan iya zama nau’in zalumci.

Ina son mutane su gane cewa a ka’idar jami’ah; ba laifi ba ne Malami yayi soyayya da dalibar shi mace.

Malamai da dama sun yi soyayya da daliban su mata har sun yi aure har da y’ay’a.

Ko a jami’ar da nake aiki an yi irin wannan aure da dama kuma Allah ya albarkace su da zurri’ah.

Ita Jami’ah babban wajibine gareta ta kare hakkin dalibai da Malamai daga cin zarafi kowanne iri ne, saboda haka tilas ne hukumar Jamiah ta tabbatar da cewa ba tilas ko barazana aka yi wa daliba ko dalibi ba.

Idan ko babu tilas cikin abunda ya faru; shikenan magana ta zama zabin mutane biyu masu hankali.

Bisa shekarun da na yi ina aiki a jami’ah na san cewa ba lallai ne irin wannan halayya ta nema tsakanin Malami da daliba ya zama laifin Malamai kadai ba.

Su ma dalibai mata suna taka rawa mai yawa wajen gabatar da kawunan su wajen Malaman na su.

Hakanan kuma yadda dalibar kan iya yarda da Malamin shi ma Malamin kan iya yarda da dalibar.

Sannan wannan video ya nuna cewa dalibar ta kai kan ta ne da niyyar Jan hankalin Malamin, sannan ta yi sintiri wajen shi har sau uku, duk abunda ya fada tana amincewa da shi, ina gani ko Sarkin gari ne za’a iya kamawa a wannan yanayi ba Malami kadai ba.

To ta yaya wannan video zai zama cikakkiyar hujja akan Malamin? Sai dai a kama shi da laifin “abusing office” amma sexual harassment kam ina ganI yarinyar ce ta bashi kofa, Lamar yadda dama mun San cewa manufar ta kenan.

Saboda haka ina bada shawarar cewa yadda aka samu yan jarida suka yi kyakkyawan bincike akan yadda wasu Malaman jamiah ke amfani da damar su wajen bata yara mata, akwai bukatar irin wannan bincike wajen gano shin dalibai matan ma kan iya haddasa irin wannan halayya

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×