Kannywood

Hirar Hadiza Gabon: Ban taɓa yin soyayya da Rakiya ba, in ji Hamisu Breaker

Shahararren mawakin soyayya na Hausa, Hamisu Breaker, ya bayyana cewa babu wata alaƙa ta soyayya da ta taɓa shiga da tsakanin sa da jarumar fim ɗin Hausa, ƴar ƙasar Nijer, Rukayya Yusuf.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ƙarshen makon nan ne dai Hadiza Gabon, fitacciyar ƴar fim ɗin Kannyywood, a wani shirin hira-da-baƙo da take gabatarwa a tashar Arewa24, ta tattauna da Rukayya Yusuf, wacce a ka fi sani da Rakiya.

A hirar, Rakiya ta bada labarin soyayyar su da Breaker, da irin wahalar da ta sha a soyayyar, a wani yanayi mai ban tausayi, inda har ta fashe da kuka yayin bada labarin a cikin shirin.

Wannan hira ta Rakiya ta haifar da cecekuce a kafafen sadarwa, musamman ma Facebook, inda har wasu da su ka kalli shirin, ke cewa suma sai da su ka zubar da hawaye sabo da tausayi.

Sai dai kuma a wani martani da Breaker din ya yi a shafinsa na Twitter, ya ce shi bada shi ta yi wannan soyayyar da ta bada labari a shirin na Gabon ba, sai dai idan da wani can ta yi.

Ya ƙara da cewa bashi da wata alaƙa da jarumar ta soyayya sai dai ta mutumci.

“Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lfy dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan batun da yake ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar Asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tayi hira da ita wasu mutane na cewa wai dani tayi soyayya kuma har na juya mata baya.

“Sam Sam wanna maganar ba haka take Hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai Mutunci,” in ji Breaker.

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa mai yuwa an zaci Hamisu Breaker din ne saurayin da ta bada labarin ya wahalar da ita, duba da cewa sun yi wakoki tare.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×