Labaran Duniya

Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Kashi 60 Na kudin Aikin Kidaya

Karamin ministan kasafin kudi da tsare tsare na nigeria clem agba ya bayyana damuwar sa kan tasirin da rashin kudi da kuma matsalan tsaro a kasar nigeria
Ya bayyana cewa an tsara gudanar da aikin kidayar ne a ranar 29 ga watan March zuwa biyu ga watan April na shekarar 2023.

Mista agba ya bayyana hakan ne ranar litinin a waya ganawa da yayi da kungiyoyi masu zaman kansu a Abuja.

Ya Kara da cewa gwamnatin tarayya ta fitar da fiye da Kashi 60 cikin 100 na kudaden da za ayi aikin Kidayar da shi.

Yayinda yace yanzu ana jiran kungiyoyi masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki da su bayar da nasu kason

Wannan ganawar dai itace ta biyu da akayi da jami’an hukumar Kidaya ta kasar keyi da kungiyoyin da zasu taimaka wajen gudanar da Kidayar jama’ar

Babban dalilin da yasa ake ganawar shine yadda za a Samar da kudin gabatar da Kidayar
Inda hukumar tayi alkawarin gudanar da komai a bayyane

Duk da hukumar tace an Sami matsalolin tsari a lokacin gwajin da akayi a wasu kananan hukumomin kasar,

Shugaban hukumar Kidayar ya kawar da fargabar da wasu keyi na cewa ba za ayi aikin a wasu sassan kasar ba

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×