
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya nemi zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya saka masa goyon bayan da ya masa na zama shugaban kasa ta hanyar mayar da dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, watau Iyan Zazzau, Hon. Abbas Tajudeen A matsayin kakakin majalisar wakilai.
Hon. Abbas dai yana wakiltar Zaria ne a majalisar ta wakilai.