News

Gaskiyar: Ba na shaye-shaye, inji Alhassan Kwalle

Ya zama ambasadan NDLEA
SHUGABAN Ƙungiyar Jaruman Hausa ta Nijeriya (Hausa Actors Guild of Nigeria), reshen Jihar Kano, Malam Alhassan Aliyu Kwalle, ya bayyana cewa shi ba ya shan miyagun ƙwayoyi ko wani abu mai sa maye.
Ya faɗi haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim a yau kan naɗa shi jakaɗe da Hukumar Yaƙi Da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta yi masa.Kamar yadda fimmagazine na ruwaito.
An naɗa Kwalle wannan matsayin ne a lokacin bikin Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi wanda hukumar ta shirya tare da haɗin gwiwar Jami’ar Bayero, Kano, a jiya Asabar, 26 ga Yuni, 2021.
A hirar sa da wannan mujallar, Kwalle ya ce, “Wani zai ga ya samu wannan damar domin ya kai ga wata manufa ko wani gaci da ya ke son ya kai, to sai ni na ke kallon tunda har aka tabbatar da cewar ni mai hankali ne kuma aka tabbatar da cewar ba na shaye-shaye sannan kuma ake ganin zan iya taimaka wa al’ummar mu wajen ganin an daina wannan sha da fataucin ƙwayoyin da sauran kayan maye.
Karanta kuma  Yadda Hadiza Gabon ta zama Uwar Marayu
“Wannan matsayi ya nuna cewar ba na shaye-shaye, in ma ina shaye-shaye in daina, ballantana Allah ya taimake ni ma ba na yi.
“Wannan zaburarwa ce aka yi mani. Su kan su abokan sana’a ta ya kamata a ce sun yi la’akari da haka saboda ba ni kaɗai aka yi wa wannan naɗin ba, don a cikin ɗimbin mutane aka zaɓo ka aka yi maka wannan naɗi ai ka ga ba ƙaramar nasara ba ce.”
Fitaccen jarumin ya bayyana farin ciki bisa wannan cigaba da ya samu, ya ce wannan naɗi wata manuniya ce ta irin zaman lafiya da kuma aiki tuƙuru a tsakanin sa da jama’a har ma da abokan sana’ar sa.

Ya ce, “Ina gode wa Allah da kuma abokanan sana’a ta da ke cikin wannan masana’anta. Sun ba ni gudunmawa ɗari bisa ɗari ta fannin yadda zan tsaya wajen gabatar da ayyukan shirye-shirye da su kan su masu kallon mu bisa yadda su ke nuna ƙwazo da gyararrakin da su ke yi mani, domin da wannan ne na samu wannan nasara har na kai ga wannan hukuma wanda shiga aikin su ma sai ka yi da gaske.

Karanta kuma  Ina tunanin tsayawa takara 2023 ~ cewar Rukayya Dawayya
“A yanzu Allah ya kawo mu wani ƙadami wanda ko naɗin sarauta za a yi maka ko muƙamin gwamnati za ka samu sai an je an auna ƙwaƙwalwar ka a ga cewa ka na shaye-shaye ko ba ka yi.

“Cikin taimakon Allah aka ɗauke ni aka yi mani wannan ambasada na wannan hukuma. Ba ni da abin da zan ce da Allah sai godiya.”

Shugaban ya ƙara da cewa wannan naɗi da aka yi masa ya zame masa wata igiya tare da ƙara zage damtse wajen yin aiki tuƙuru don ƙara daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin jarumai.

Shugaban ya yi kira ga ‘yan fim da su maida hankali wajen zama da kowa lafiya da yin mu’amala tagari a tsanin al’umma.

Ya ce, “A har kullum ina gaya wa jama’a da abokanan sana’a ta cewa mu a masana’antar nan mun gode wa Allah, saboda ba wai ka zo ka fara sana’a ka yi suna ko ka yi kuɗi ba shi ne abin nema ba.

Karanta kuma  Hukumar Hizba A Kano Ta Umarci Matashin Da Aka Yi Wa Kwal-kwal Yin Sallah Raka’a 100
“Wannan wani abu ne in ka samu sai ka gode wa Allah, amma babban abin da ake so a ko’ina ka tabbatar da cewa wanene kai? Daga ina ka fito? Kuma ka na yi ka na waige ka ga daga ina ka fito.

Abin da na ke nufi a nan shi ne ba wai an naɗa ka a ambasada na mai wannan sana’ar fim ba, a’a, ambasada ne na al’ummar ka ta Hausawa kuma ambasada ne kai na addinin ka, don haka idan da ba mu da mutunci ba za mu samu wannan damar ba.”

Ban da Kwalle, wasu daga cikin jarumai da su ma aka naɗa su jakadun hukumar sun haɗa da Shehu Hassan Kano, Hankaka, Bashir Bala (Ciroki) da Ruƙayya Dawayya.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×