Kannywood

Duk Wanda Na Yiwa Addu’a Sai Allah Ya Karɓa -Saratu Gidado

Fitacciyar jaruma a masana’antar Kanywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso ta bayyana cewa tana da wata baiwa ta musamman da Allah ya yi mata, wacce kuma mutane ba su san tana tare da wannan baiwa ba.


Saratu Gidado ta bayyana hakan ne a cikin wani shiri da gidan rediyon BBC Hausa ya ke gabatarwa mai suna Daga Bakin Mai Ita.

Jarumar ta ce lokaci ya yi da ya kamata duniya ta san tana tattare da wannan baiwa.
Tun da farko masu gabatar da shirin sun yi mata tambaya shin ko tana da wata baiwa ta musamman? Sai Saratu Gidado ta kayar da baki ta ce

“Eh akwai baiwa da Allah ya yi min da ba kowa ya sani ba, amma yanzu zan so duniya ta sani baiwar ita ce: gaskiya idan har na yiwa mutum addu’a, in har na yiwa mutum addu’a In Sha Allahu da izinin Allah tana karɓuwa”
Jaruma Daso ta bayyana cewa ita ba ta dauki shirin fim wani abu da zai zama hanyar fadakar da mutane ka koya musu tarbiyya, a’a ta dauke shi ne kawai a matsayin kasuwanci.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu jaruman ke ikirarin shirin su na fim na koyarwa da al’umma tarbiyya tare da fadakarwa

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×