Videos

Duk Masoyin Adam A Zango Bazai So Rabuwar Sa Da Safiya Chalawa Ba Duba Da Zargin Auri Saki Da Ake Aura Masa

20230209 154805

Kamar yadda aka yi tsammäni ne maganganu ne ta ko’ina Zango zai sha su kan halin da ya ke ciki da matar tunds har ya fito da shi media wanda tuni kurar sa tayi kuka kan batun auri saki da ake masa wanda kuma sanin Keane Gandaki shi yasan inda vake masa.

Labarai na abin da Zango bai fito ya fadi ba sun fi wanda ya fadi duk da yawan maganar shi wanda duk wasu abubuwa da bayyana game da Safiya chalawa masu sauki ne akan wasu daga matan da ya saki wanda ni a ganina zai iya jure wannan inda har ya tuna da abubuwan da suka faru a baya kan sauran matan sa kamar yadda ake fada wasu abubuwan sai dai balsu daulance daudar gora a ciki ake shanye ta.

Wata majiya ta bayyana mana a cikin matan da zango ya taba saki hadda wacce ke wata mu’amalar a cikin auren shi da wacce ta kawo masa barayi gida da sauran su kaga ko dan ta Safiya uwar Adashi mai sauki ce sai dai in akwai kuma wani abu da bamu sani ba wasu masu hikima na cewa kowacce mace ciwon kai ce sai dai kawai ka zabi wacce zaka shawa magani amma duk kanwar ja ce haka ma kuma yake kmazan gabadaya auren dan hakuri ne.

Sai dai duk da haka zangon bazai kubuta daga zargin mutane ba kasancewar wannan shine aure na kusan shida idan ya rabu da safiya wanda wasu na cewa har a cikin dangi yayi auren an rabu a yan film din ya aura ba’a dace ba wannan karon da ya auro karamar yarinya mai karancin wayewa ma dai ba’a tsira ba dole wasu zasu tattara laifin akan shi gaba daya dukda wani sa’ilin ana samun rashin dace kuma duk adadin matan da Allah ya rubuta akwai rabo a tsakanin ku sai ka gula dan mata bazata haifi dan wata ba.

 

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×