Labaran Duniya

Dubun wani Magidanci mai basaja a matsayin Mace An tasa ƙeyarsa zuwa Gidan Gyaran hali

Magidancin da ya ke basaja a matsayin Mace ya samu gurbi a gidan gyaran


Dubun wani Magidanci mai basaja a matsayin Mace An tasa ƙeyarsa zuwa Gidan Gyaran hali

Wani magidanci a jihar Adamawa, Muhammed Abubakar mai shigar kayan mata ya na neman kudi a hannun mutane ya shiga hannun hukuma kamar yadda dalafim na kawo rahoto.

Muhammed, wanda ya yi Diploma kan harkokin kasuwanci daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa, Yola, ya ce ya na yin ado kamar mace kuma ya na bin mata da sunan shi mace ne.

Muhammed wanda dan asalin garin Tashan Sani ne a karamar hukumar Yola ta Kudu kuma mai suna Fadi, ya bayyanawa wata babbar kotun majistare dake Girei kusa da babban birnin jihar Yola cewa, ya na aiki tare da abokansa mata.

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ne bayan da dan sanda mai shigar da kara, Wamkai Ngapuro ya gurfanar da shi a gaban kotu.

An bayyana cewa bayan ya na samun kudi tsakanin Naira 500 zuwa Naira 1, 500, bisa la’akari da kudin da suke samu daga wurin maza a rana.

Babban Kotun Majistare, karkashin jagorancin Martina Gregory, bayan da ya amsa laifinsa, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari har zuwa ranar 5 ga Disamba, 2022.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×