Labaran Duniya

Bambamcin Mata Mazan Yar Maɗigo (Tomboy) Da Macen ‘Yar Maɗigo (Lesbian)

Nayi wannan rubutun ne saboda yadda mata da dama masu sha’awar daina dabiar madugo suka yi ta neman shawara ta domin rabuwa da wannan mugun halin.

Wannan yasa nayi doguwar bincike har na gano bambamcin dake tsakanin mai nema da wacce ake nema da kuma yadda za ayi su daina.

Wasu cikinsu sunyi amfani da shawarar dana basu kuma sun dace, akwai ma waɗanda yanzu haka suna Gidajen mazansu kuma suna zaune lafiya harma da samun karuwa.

Da fatan masu karatu da dalibai Tsangaya zasu amfana da wannan rubutun.

Matan mazan mace wacce a turance ake kiransu Tomboy, da kuma Macen yar madugo da ake nemanta wacce ake kira Lesbian a turance, dukkaninsu mata ne a zahirance sai dai ita Tomboy wacce itace namijin bata daukan kanta a mace,.

Kuma ita haka take tasowa da ɗabi’a irin na maza kamar yadda ‘yan daudu suke tasowa (zamu yi karatun nan gaba) .Bambamcin Mata Mazan Yar Maɗugo (Tomboy) Da Macen 'Yar Maɗugo (Lesbian)

Ita dai Mata mazan mace, wato mace ce mai daukan kanta tamkar namiji.

Gata dai a zahiri mace ce duk kuwa da ana samun wasu da dama masu kiran maza har muryarsu irin na maza.

Amma su a zuciyarsu da Ɗabi’ar su suna daukan kansu tamkar namiji. Hakan yasa ma gani suke yin soyayya da namiji tamkar namiji ne da namiji don haka mafi yawan irin waɗannan matan basa sha’awar maza sai mata. Saboda suna daukan kansu suma maza ne. Duk wani hidima da namiji zai Yiwa mace suma hakan suke yi.

Ga kabilun cikinsu ko turawa ba za a taba ganin su sunyi shiga irin na mata ba, kullum cikin wando ko shiga irin na maza suke yi. Wani lokacin ma har auren junansu suke yi a zhirance. Sai dai irin waɗannan alamun bazaka cika ganin su a zihiri cikin matan mazan Hausawa ba saboda al’ada da addini da suka hanasu shiga irin na maza a fili da kuma basu da damar auren junansu. Duk kuwa da akwai su da damar gaske. Amma kuma suna nuna soyayyar su matuka ga duk macen da suka kyalla idanuwa suka ji suna Sonta.

Mazan matan yar Madigo tafi macen yar madugo illa matuka a rayuwar. Saboda ita sai an dace da daukar wasu matakai masu tsauri kuma dole sai ta bada haddin kai za a iya cimma wannan burin na samun nasarar dainawar ta saboda akasarinsu tun suna ƙananansu iyayen su suka yi sakaci wajen nuna rashin kula da yadda suka taso da halaye irin na maza ba tare da sun gyara su ba ko sun nuna musu bambamce bambamcen dake tsakanin mace dana miji ba.

A rubuce rubuce na baya nayi bayanin wasu dalilan da suke sa mace ta soma aikata maɗugo cikinsu harda haduwa da Matan Mazan wanda suke yaudararsu da hanyoyi mabambamta wajen jawo hankalin su shiga wannan harkar.
Mata maza yar maɗugo basu da kunya ko tsoro nuna halinsu a zahiri muddin suka ga wacce suke so. Amma su wacce ake nema basu cika nuna kansu a fili ba.

Yar Maɗugo da ake nema tana sha’awar aure da haihuwa, amma ita Mata maza aure bai dameta ba barema soyayyar abunda za a haifa bayan auren. Wacce ake nema tana iya daina yin maɗugo har abada musamman idan wanda take so kuma ta aura zai iya sarrafata yadda samarinta na maɗugo suke mata.

Yana da matukar wahala matan mazan yar maɗugo tayi samari maza sai dai waɗanda zata rika samun kudi wajen su domin kashewa yan matanta.

Akasarin maza da suke mu’amala dasu ko dai kasuwanci ko aiki ya hadasu ko kuma tana daukar sa tamkar abokina ne.

Wanda ita Lesbian tana soyayya da maza don haka nema akasarin yan madugon da muke dasu bisex ne.

Maza da mata na neman su, amma ita Tomboy yin mu’amala dana miji a wajenta sai dai a dole kuma ba gamsuwa take yi ba.

Aure suna yinsa saboda rashin damar da zasu iya sakata su wala.

Haka kuma muddin suka kasa samun sararin ci gaba da kawo mata ko mu’amala da mata suna iya kashe aurensu su zauna babu auren tunda dai sun yi na farko.

Waɗannan bambamce bambamce sune a zahiri mutane zasu iya ganinsu musamman ma iyaye.

Akwai ‘yan mata dama da suke gudun aure saboda irin wannan ɗabi’ar data riga ta yi musu katutu a ransu. Amma sai iyayensu suna daukar cewa aljannu ne ko kuma sa hannun maƙiya ne na hanasu aure duk kuwa da akwai samarin dake son su da aure amma a zahiri abun ba haka yake ba.

Sai dai kada hankalin masu yi da suke son dainawa ya tashi, ko waɗanda suke da masaniyar ‘ya’yansu ko’ yan uwansu nayi amma sun kasa dainawa ransu ya ɓaci. Akwai hanyoyi da shawarwari na masana harma da malamai da suka bayar domin daina wannan ɗabi’ar.
Allah Ya daɗa karemu, Ya kuma shirya mana zuriya.
Zamu ci gaba…

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×