Kannywood

BADAKALAR KWANKWASIYYA: Gaskiya Ali Artwork Ba Shi Da Zuciya, Cewar Hauwa Farouk

Daya daga cikin shahararrun ‘yan soshiyal midiya mai suna Hauwa Farouk Ibrahim ta ce a rayuwar ta ba ta taba ganin mutum mara zuciya irin Ali Art Work ba.

Jarumin barkwancin wanda aka fi sani da Madagwal na cigaba da shan suka ne kan irin tsalle-tsallan da yake yi a siyasa.

Da shi aka yaki jam’iyar NNPP kafin zabe a Kano, amma ana bayyana Abba Gida-Gida a matsayin wanda ya lashe zabe ya kasa zaune ya kasa tsaye inda yake ta kokarin cusa kan sa a tafiyar Kwankwaso wanda ya watsar a baya.

Hakan nan kowa ya san da cewa shi na hannun daman Gwamnan Jihar Zamfara ne Matawalle amma tun randa Matawalle ya fadi zabe ya fara tallar sabon Gwamnan Jihar wanda ya kada Matawallen.

Shin kuna ganin duk da haka yakamata ace Hauwa Farouk Ibrahim, ta bayyana shi Amatsayin mara zuciya????

Daga Nuruddeen Isyaku Daza

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×