Kannywood

Ali Nuhu Dalilai 10 da yasa jarumi yazama abun koyi a masana’antarKannywood

Hakika masana’antar kannywood ta samu babban abun
al’fahari kasancewa tare da wannan jarumin a masana’antar.
 
Ga wasu dalilai 10 da muke ganin cewa sune abubuwan da
yasa yan arewa ke farin ciki gannin wannan tauraron wanda
aka wa lakabi na “sarkin kannywood” a talabijin;
1. Ya dade yana harkar fina-finai
 
Tun shekara 1999 Ali nuhu ya fara fitowa cikin fina-finai kuma
babban shirin da ya fitar dashi idon jama’a shine “sangaya”.
2. Banda Kannywood jarumin jakada ne a masana’antar
Nollywood
Wannan jarumin ya nuna mana cewa banda haushen hausa ya
kware wajen yin fina-finai cikin harshen turanci.Ya fito a cikin
shirin nollywood da dama.
3. Ya amshi lambar yabo da dama
Wannan jarumin ya amshi lambobin yabo bila adadi cikin gida
har da ƙasashen waje.
4. Shi na kowa ne
Indai ta yadda abokan hamayen shi na masana’antar zasu
samu karuwa wannan jarumin yana gaba gaba wajen tabbatar
da haka kuma sauran jaruman na alfahari kasancewa tare
dashi.
5. Yana da ƙwarjini har ƙasashen waje da masana’antu daban
daban
Hakika idan muka shiga wasu kasashe zamu ji cewa sunan Ali
Nuhu yana yaduwa sanadiyar rawan da yake takawa a wajen
yin fim.
6. A harkar fim ya nuna cewa na “Uba da ɗa” ne
Shima dai dan sa Ahmad Ali Nuhu ya fara fitowa a fina-finai
hausa tun yana dan yaro bayan ya bayyana ma uban shi cewa
shima a gaskiya yana sha’awar yin fim, ganin cewa faduwa ta
zo dai dai da zama uban ya mara masa baya amma da
sharadi na dole sai ya dage wajen koyan ilimi kuma zai dinga
yin haka idan ya samu hutu daga makaranta.
7. Da ka ganshi ka gan tambarin Arewa
Shi dai wannan jarumin baya boye ma jama’a a duk inda ya
sinci kanshi cewa shi ban dan arewa bane kuma kullum yana
neman yadda zai yada al’adar yan arewa ga sauran jama’a.
8. Suma masoyan shi suna farin ciki idan suka ci karo dashi
Ganin cewa ya shahara a fannin shirya fina-finai jarumin baya
kyamar tarbar masoyan shi a duk inda ya gamu dasu.
9. Yana son ƙwallon kafa kuma yana tare da tawagar Nijeriya
dari bisa dari
Duk wani wassan kwallo da ya danganci Nijeriya tauraron
Kannywood yana gaba gaba wajen goyon bayan tawagar kuma
aboki ne ga yan wassan super eagles.
10. Ko zamu iya cewa mutu ka raba?
A yanzu dai wannan jarumin yana da shekaru 43 a duniya
kuma ya kwashi shekara 19 yana nishatarda mu. Har yanzu
jarumin yana nuna cewa kamar yanzu ya fara wannan sana’ar
shirya fina-finai kuma ba alamun gazawa tare dashi.
Daga nan mu dai muna jinjina ma wannan ƙwararren jarumin
da ayyukan da yake yi wajen fadakarwa, nishatarwa tare da
ilmantar da mutanen Arewa.
Mun Dauko Daga Shafin 

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×