
Shugaba Buhari Ka Taimaka Mana Ka Sanya Mana Hannu A Gina Jami’a a Funtua
Daga Ibrahim Auwal Al’ja,a Funtua
Yau sama da shekara daya kenan Majalisar Dattawa ta kasa a Nijeriya ta tantance tare da amincewa da gina Jami,ar Aikin Gona da Fasaha a Funtua, wanda Sanatan Shiyyar Funtua Sanata Bello Mandiya ya gabatar.
Bayan Majalisar Dattawa ta gama tantancewa, ta aikawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Takardar domin Amincewa.
A yanzu haka Takardar na ofishin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai sanya hannu ba.
A madadin Matasa masu kishin Al,ummar Shiyyar Funtua, bisa jagorancin Malam Auwal Al’ja,a Funtua, muna koro da a taimaka a sanya mana hannu domin tabbatar da wannan Makaranta.