Uncategorized

Abubuwan da ya rage bayan yankewa Abduljabbar Kabara hukuncin Rataya

An dai shafe sama da shekara guda ana dambarwa da kai komo kan wannan shari’a kafin a kai wannan matsayi a yanzu

Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai na zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa’azinsa.

Sai dai kafin yanke hukuncin a jawabinsa na ƙarshe, Sheikh Abduljabar ya yi ikirarin cewa lauyan da ya nemi afuwa a madadinsa bai san shi ba kuma bai taɓa ganinsa ba.

To ko mene ne abu na gaba da ya rage wa Sheikh Abduljabar? Usman Mai Keke Lauya ne mai zaman kansa a jihar Kano, kuma ya shaida wa BBC cewa zaɓi biyu suka ragewa malamin a wannan gaɓar.

Abubuwan da ya rage bayan yankewa Abduljabbar Kabara hukuncin Rataya
Abubuwan da ya rage bayan yankewa Abduljabbar Kabara hukuncin Rataya

Tun bayan sanar da hukuncin rataya kan fitaccen malamin Islama Sheikh Abduljabar Nasir Kabara da wata Kotun Shari’ar Musulunci ta yi a Kano, kusan abin da ake tattaunawa shi ne mene ne abu na gaba bayan yanke hukuncin.

A wannan Alhamis din babbar kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta samu Sheikh Abduljabar da laifin yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.

Kotun ta ce bayan dogon nazari kan abubuwan suka wakana a gabanta bisa dogaro da hujjojin litattafan Musulunci da Hadisai ne, aka yanke masa hukuncin.

Daukaka ƙara ko zaman jiran aiwatar da hukunci’

Barista Usman ya ce bisa tanadin dokoki da kudin tsarin mulki na Najeriya duk wani wanda aka yanke wa hukunci na da damar ɗaukaka kara zuwa kotu ta gaba domin ƙalubalantar shari’ar bisa hujojji masu ƙarfi.

Sai dai kuma ana iya aiwatar da hakan bisa wasu kwanaki da aka tanada, kuma da zarar mutum ya wuce waɗannan kwanaki babu batun ɗaukaka ƙara, sai kuma jiran zartar da hukunci.

Amma kuma abu na biyu idan ya ɗaukaka kara bisa wasu dalilai da zai ambata, kotu za ta dubi waɗannan dalilai da kuma yadda aka gudanar da shari’ar.

Idan an tabbatar an sauka daga kan layi ko akasin haka ana iya gyaran fuska kan shari’ar.

Amma kuma idan kotu ba ta gamsu da hujojji ko dalilai ko bayanai da aka gabatar ba, to za ta sake jaddada hukuncin farko.

Sannan lauyan ya ce malamin yana da damar roƙon kotu ta ƙara masa lokacin daukaka ƙara, idan kuma har ya zauna jinkiri har kwanaki suka cika shikenan.

“Ita kotu aikinta sauraron kowanne ɓangare ta faɗi ra’ayinta, idan kotu ta yanke irin wannan hukunci kuma da ya shafi rai, gwamna ke da iko na ƙarshe.

“Domin idan alkali ya yanke hukuncin rataya dole sai gwamna ya sanya hannu kafin a yi wannan hukunci, ba wai kawai kai-tsaye za a aikata ba,” in ji Barista Usman.

Barista Usman ya ce in dai aka cike waɗannan ƙa’idoji to babu wani laifi da ya saɓawa kudin tsari ko dokokin ƙasa.

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×