Kannywood

Ƴan Kannywood sun koka bisa ƙin saka su a kwamitin rantsuwa na Tinubu

 

fim ta kudancin Nijeriya, wato Nollywood a kan ƴan Arewa, musamman fitattun jaruman Kannywood.

A cewarsa, abin mamaki ne a ce fitattun ƴan Kannywood irin su Mansura Isah, Ali Nuhu, Abdul Amart, Jamila Nagudu da sauransu, ba su samu shiga cikin jerin sunayen ba, duk da cewa sun yi iya bakin kokarinsu a yakin neman zaben jam’iyyar APC a Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, “mafi yawan wadanda suka shahara a masana’antar fina-finan Hausa, sun yi yakin neman zaben Tinubu tun kafin babban taro.

“Tuni dai mashahuran ƴan Kannywood irin su Mansura Isah sun shahara wajen yiwa ‘Jagaban’ yakin neman zabe tun kafin a bayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.

“ni kuwa ina tambayar kwamitin rikon kwarya na Asiwaju me ya sa aka kafa shi ba tare da wani fitaccen dan Kannywood ko daya a jerin sunayen ba?

Sanarwar ta kara da cewa “Yawancin jaruman Nollywood da aka sanya a cikin jerin ba su ma nuna fuskokinsu ba a lokacin yakin neman zabe da zabe.”

Mr.Bangis

Take Your Time And Come Back Strong!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
×